Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da wani zama kan mu'ujizar kur'ani mai tsarki da kuma sunnar manzon Allah (SAW) a birnin Jazan na kasar saudiyya, tare da halartar malamai dam asana.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an nasij an bayyana cewa, an fara gudanar da wani zama kan mu'ujizar kur'ani mai tsarki da kuma sunnar manzon Allah (SAW) a birnin Jazan na kasar saudiyya, tare da halartar malamai da masana daga sassa na kasar da ma kasashen ketare.
Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da wannan zaman taro ita ce yin nazari kan muhimman abubuwa da kur'ani ya yi ishara da su da suke tabbatar da cewa shi littafi ne daga mahaliccin kowa da komai.
Yanzu haka dai mahalarta taron suna ci gaba da sauraren bayanan da ake gabatarwa tare da karbar makaloli da manyan malamai gami dam asana da malaman jami'oi suka rubuta kan hakan.
Haka nan kuma a bangare guda taron yana yin dubi kan koyarwar manzon Allah (SAW) da yin aiki da sunnarsa a cikin dukkanin bangarori na rayuwa.
682182