IQNA

Kungiyar Hizbullahi Ta Yi Allah Wadai Da Ta'addancin Amerika A Iraki

10:47 - October 27, 2010
Lambar Labari: 2020642
Bangaren siyasa da zamantakewa: bayan bayyana bayanan sirri kan harin da Amerika ta kaddamar a Iraki da Wikileaks ta fitar kungiyar gwagwarmaya ta hizbullahi a kasar Labanon ta fitar da bayani da a cikinsa take yin Allah wadai da ayyukan ta'addanci da assha da sojojin amerika suka aikata a Iraki da kuma yadda suka azabtar da fararen hula.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran daga reshenta da ke kasar Labanon ya watsa rahoton cewa; bayan bayyana bayanan sirri kan harin da Amerika ta kaddamar a Iraki da Wikileaks ta fitar kungiyar gwagwarmaya ta hizbullahi a kasar Labanon ta fitar da bayani da a cikinsa take yin Allah wadai da ayyukan ta'addanci da assha da sojojin amerika suka aikata a Iraki da kuma yadda suka azabtar da fararen hula. A cikin wannan rahoto na sirri an bayyana wasu daga cikin dubban abubuwan assha da sojojin Amerika suka tabka a kasar Iraki kan fararen hula da kuma yadda suka yi kisan gilla da azabtar da fararen hula hankali kwance babu tausayi da face halin dabbanci karara.






682714
captcha