Bangaren kasa da kasa, An gudanar da tarukan girmama mutanen da suka karbi addinin muausulunci ba da jimawa ba wadanda suka gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar Malazia, wanda aka gudanar a birnin Kualalampour.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na Iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bernama an bayyana cewa, an gudanar da tarukan girmama mutanen da suka karbi addinin muausulunci ba da jimawa ba wadanda suka gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar Malazia, wanda aka gudanar a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin wadanda suka shiga wannan gasa mutane ne da suka karbi addinin muslunci a matsayin addinin da suka yi imani da gaskiyarsa da kuma amincewa da sakon da yake dauke ga dukkanin bil adama.
An gudanar da bukin tare da halartar manyan jami'an gwamnati da suka hada da fira ministan kasar da kuma mai dakinsa, tare kuma da halartar fitattun makaranta kura'ni mai tsarki na kasar su kimanin casa'in da takwas.
682853