Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da wani gwaji na wata sabuwar tashar Musulunci da aka bude a kasar malazia da aka baiwa suna hijrat, wadda za ta rika watsa shirye-shirye na addinin Musulunci daga kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na Bernama na yanar gizo an bayyana cewa, an fara gudanar da wani gwaji na wata sabuwar tashar Musulunci da aka bude a kasar malazia da aka baiwa suna hijrat, wadda za ta rika watsa shirye-shirye na addinin Musulunci daga birnin Kualalampour fadar mulkin kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka wannan sabuwar tashar talabijin tana watsa wasu daga cikin shirye-shirye na gwaji, da nufin samun damar isar da sakonnin Musulunci ga mutanen da musamman ba musulmi ban e.
Babbar manufar bude tashar ita ce kara wayar da kan musulmi da kuma sauran mutanen da sue da sha'awar sanin wani abu dangane da koyarwar addinin muslunci, kan batutuwa na raywar zamantakewa.
682786