Bangaren kasa da kasa, An bude taron baje kolin littafan addinin muslunci a birnin Mumbai cibiyar kasuwanci ta kasar India, wanda yanzu haka zuba littafai daban-daban da suka haura dubu 10 a wurin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar iqtisadiyya ta kasar Saudiyya an habarta cewa, an bude taron baje kolin littafan addinin muslunci a birnin Mumbai cibiyar kasuwanci ta kasar India, wanda yanzu haka zuba littafai daban-daban da suka haura dubu 10 a wurin da ake gudanar da baje kolin.
Bayanin ya ci gaba da cewa baje kolin yana samun halartar cibiyoyin ilimi na musulmi da suke cikin kasar daga sassa daban-daban da suke baje kolin abubuwan da suke bugawa da nufin yada addinin muslunci a tsaknain al'ummomin kasar.
Sama dam asana da kuma marubuta 2500 ne suke halartar wannan baje koli, daga cikin abubuwan da ake nunawa ban da littafai hard a wasu daga cikin kayayyakin fasaha na Musulunci da suka da alluna da suke dauke da rubutu.
682768