Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; binciken yadda za a bunkasa dangantakar musulmi da kiristoci a wani zama manema labarai na kasa da kasa karo na goma sha bakwai.Masu gudanar da wannan zama na kokarin samar da hanyoyin da za su ga sun inganta duk wata dangantaka da hanyar da za ta taimaka wajen kusanci tsakanin musulmi da kiristoci a fadin duniya .Wannan taro an gudanar da shi ne a dakin gudanar da taro na babban masallaci.Kuma gudanar da irin wannan taro ko shakka babu zai taimaka matuka gaya wajen kara kusanci a tsakanin musulmi da kiristoci a fadin duniya ba wai kawai a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran.
683544