IQNA

An Nuna Mujallar Hadin Kai A Baje Kolin Kayan Sadarwa

16:56 - October 28, 2010
Lambar Labari: 2021316
Bangaren kasa da kasa, An nuna wata sabuwar mujalla da ake bugawa a kasar Oman da ke yin kira zuwa ga hadin dukkanin al'ummar musulmi, a baje kolin kasa da kasa da ke gudana a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zanatawa da ta hada shi da shugaban bangaen isar da sakon muslunci na ma'aikatar kula da harkokin addini ta Iran ya bayyana cewa, an nuna wata sabuwar mujalla da ake bugawa a kasar Oman da ke yin kira zuwa ga hadin dukkanin al'ummar musulmi, a baje kolin kasa da kasa da ke gudana a birnin Tehran.

Babban daraktan bangaren yada addini na ma'aikatar kula da ayyukan addinin muslunci na kasar Oman Khalid Bin Sa'id Almushrifi ya bayyana cewa, wannan baje koli na daya daga cikin muhimmai irinsa da ya taba halarta.

Ya ci gaba da cewa mujallar hadin kai da suke bugawa a kasar Oman tana da burin ganin cewa an samu hadin kai tsakanin dukkanin bangarorin na al'ummar musulmi baki daya a duk inda suke cikin duniya.

683647
captcha