Bangaren kasa da kasa, A bangaren kyayyakin mudala'a na baje kolin da ake gudanarwa a hubbaren marigayi Imam Khomeni da ke cikin birnin Tehran, an nuna wasu daga cikin rubuce-rubucen da malamai Irakawa suka yi kan harkokin sadarwa a kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wanilabari da ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na cibiyar Agura an bayyana cewa, a bangaren kyayyakin mudala'a na baje kolin da ake gudanarwa a hubbaren marigayi Imam Khomeni da ke cikin birnin Tehran, an nuna wasu daga cikin rubuce-rubucen da malamai Irakawa suka yi kan harkokin sadarwa a kasashen musulmi baki daya.
Wannan bangare ya nuna wasu daga cikin mujallun da ake bugawa akasar Iraki, da masana gami da malaman addinin muslunci na kasar sukan yi rubuce-rubuce a cikinsu domin fadakar da musuli da kuma yi musu hannuka mai sanda kan harkokin rayuwa da kuma zamantakewa.
Daga cikin abubuwan da bangaren nuna rubuce-rubucen malaman irakawa ya nuna hard a wasu daga cikin abubuwan da marigayi Imam Khomeni(RA) ya rubuta a lokacin rayuwarsa, da kuma wasu daga cikin littafan Shahid Mottahari.
683602