Bangaren kasa da kasa, Za a kafa bankin muslunci na farko a tsibirin Maldiv, tare da hadin gwiwa da bankin muslunci na kasar Malazia IBFIM wanda shi ne babbn bankin muslunci a cikin kasashen musulmi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bernama cewa, za a kafa bankin muslunci na farko a tsibirin Maldiv, tare da hadin gwiwa da bankin muslunci na kasar Malazia IBFIM wanda shi ne babbn bankin muslunci a cikin kasashen musulmi da na larabawa.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan banki da za a kafa a kasar Maldiv zai baiwa musulmi masu bukatar saka hannayen jari a bankunan muslunci damar saka hannayen jarinsu a cikinsa, tare da karfafa tattalin arzikin kasashen musulmi da kuma kamfanonin musulmi.
An bijiro da wannan shawara ne a zaman da jami'ai kan harkokin kudi da bankuna na kasashen musulmi suka gudanar a birnin Kualalmpour na kasar Malzia, inda aka amince da kafa bankin muslunci a tsibirin Maldiv tare da hadin gwiwar bankin Malazia.
683495