IQNA

Shahararrun Mata A Nahiyar Turai Na Karbar Addinin Muslunci

16:55 - October 28, 2010
Lambar Labari: 2021320
Bangaren kasa da kasa, Cibiyar bincike ta YouGov ta kasar Birtanitaya, ta fitar da wani rahoto bayan gudanar da bincike da ta yi da ke cewa, fitattun mata a cikin nahiyar turai na karbar addinin muslunci a cikin 'ya lokutan nan.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Zaman an bayyana cewa, cibiyar bincike ta YouGov ta kasar Birtanitaya, ta fitar da wani rahoto bayan gudanar da bincike da ta yi da ke cewa, fitattun mata a cikin nahiyar turai na karbar addinin muslunci a cikin wadannan shekaru.

Rahoton ya ce irin yadda addinin muslunci ke samun saurin karbuwa a cikin kasashen turai na da ban mamaki, musamamn ga mata wadanda suka yi fice a cikin harkoki na duniya, wanda hakan ke tabbatar da cewa hankoron bata surar muslunci a cikin nahiyar turai dai bai yi nasara.

Abin da ya faru a cikin 'yan makonin nan na musluntar 'yar uwar matar tsohon fira ministan kasar Birtaniya Tony Blair ya tabbatar da cewa addinin muslunci yana samun karbuwa.

683528



captcha