Bangaren kasa da kasa masana sattin da marubuta da manazarta,masu rajin kare hakkin dan adam day an siyasa daga kasashen Saudiya,Katar,Koweiti, Oman da Bahrain sun fitar da wani bayani na hadin guiwa da suke kalubalantar duk wata fitina ta kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin musulmi da siyasar nuna banbanci da wariya da kawo karshen wannan matsala.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; masana sattin da marubuta da manazarta,masu rajin kare hakkin dan adam day an siyasa daga kasashen Saudiya,Katar,Koweiti, Oman da Bahrain sun fitar da wani bayani na hadin guiwa da suke kalubalantar duk wata fitina ta kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin musulmi da siyasar nuna banbanci da wariya da kawo karshen wannan matsala. A cikin wasikar sun bukaci girmama hakkin dan adam,karamar dan adam da yancin dan adam.
686482