Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga jaridar Today's Zaman ya watsa rahoton cewa; China na kokarin ganin ta fadada dangantakarta da kuma kyautatata a tsakaninta da duniyar musulmi da hanakan zai fata damar kara samun masaniya da al'ummar musulmi a ciki da wajen kasar ta China.Muhimmat Gurmaz mukaddashin ofishin da ke kula da harkokin addini a Turkiya wanda a matsayinsa na wakilin kasar turkiya tare da takwarorinsa goma daga kasashen Sudan,Sadiya,Koweiti,Jodan,Bosniya da suka amsa bukatar kungiyar hadin kan kasashen musulmi suka ziyarci Cana sun bayyana cewa; mahukumatan Cana na kokarin ganin sun inganta dangantakarsu da duniyar musulmi da kuma neman hanyar warware matsalolin da musulmi mazauna wannan kasa ke ciki.
686391