Bangaren kasa da kasa; ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiya a jiya ne ashirin da biyu ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira kamariya ta yi Allah wadai da matakin haramtacciyar kasar Isra'ila na gina matsugunnan yahudawa yan share gurin zauna a kewayen birnin Kudus.