IQNA

Jirgin Kasa Na Farako Na Aikin Hajji A Makka Za A Kaddamar

Bangaren kasa da kasa;a karon farko za kaddamar da jirgin kasa na aikin hajji ga maniyatan aikin hajin bana a gurare masu tsarki domin sauwake aiki kamar a Mina Muzzalifa,Arafat da wajen jifan Shaidan kuma jiya ne aka gudanar da bukin kaddamarwar da kuma fara aiki da shi a yau.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; a karon farko za kaddamar da jirgin kasa na aikin hajji ga maniyatan aikin hajin bana a gurare masu tsarki domin sauwake aiki kamar a Mina Muzzalifa,Arafat da wajen jifan Shaidan kuma jiya ne aka gudanar da bukin kaddamarwar da kuma fara aiki da shi a yau. A kowace awa guda zai yi jigilar mahajjata dubu dari daga wannan guri zuwa wancen guri kuma kimanin mahajjata dubu dari da saba'in da biyar ne zai ji jigilarsu da wannan adadi ya kasance kashi talatin da biyar cikin dari na mahajjatan bana.


694208