IQNA

Kawo Karshen Gasar Hardar Hadisi Ta Kisa'a A Haramin Muttahar Na Imam Huseini (AS)

Bangaren kasa da kasa; gasar hardar hadisin Kisa'a musamman ga yara kanana daga kasashe daban daban na Larabawa da aka fara tun ranar ashirin ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a Haramin Imam Husein (As)



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Nun ya watsa rahoton cewa' gasar hardar hadisin Kisa'a musamman ga yara kanana daga kasashe daban daban na Larabawa da aka fara tun ranar ashirin ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a Haramin Imam Husein (As). Kimanin yara kanana dubu daya ne daga kasashen iraki,Saudiya,Oman, Da Bahrain ne suka taru domin fafatawa da junansu a cikin wannan gasar karatun kur'ani mai girma.


695463