Bangaren kasa da kasa; Jam'iyar Die GRiinen a kasar Jamus ta bukaci gwamantin kasar da ta gaggauta koyar da darussan addinin Musulunci a makarantun gwamnati a fadin jahar Nur darayin Vastalon.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta dunyabulteni ya watsa rahoton cewa' Jam'iyar Die GRiinen a kasar Jamus ta bukaci gwamantin kasar da ta gaggauta koyar da darussan addinin Musulunci a makarantun gwamnati a fadin jahar Nur darayin Vastalon. Kungiyoyi da daman e suka sha yin irin wannan kira da gabatar da bukata da ta biyo bayan irin wannan bukata da shugabannin da musulmi yan kasar ta Jamus ko mazauna kasar suka gatara na bawa yayansu damar samun ilimin addinin Musulunci a fadin kasar.
695367