Bangaren kasa da kasa: a ranar sha shida ga watan azar ne na wannan shekara ta dubu daya da tamanin da tara a ranar farko ta watan muharram za a bude radiyon yada Musulunci a birnin Makka mai tsarki.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta spa ya watsa rahoton cewa; a ranar sha shida ga watan azar ne na wannan shekara ta dubu daya da tamanin da tara a ranar farko ta watan muharram za a bude radiyon yada Musulunci a birnin Makka mai tsarki.Wannan radiyo na yada addinin Musulunci an kafa shi ne zummar yadda addinin Musulunci da tilawar karatun kur'ani mai girma daga kwararru dam asana kira'ar kur'ani da suka yi fice a duniyar musulmi.Har ila yau wannan radiyo zai rika watsa shirye-shiryensa a cikin sa'o'I ashirin da hudu.
696188