IQNA

Za A Kaddamnar Da Reshen Jami'ar Azzahar Da Zummar Yada Musulunci A Turai

Bangaren kasa da kasa: Ahmad Khatib Shekhul Azzahar ya bada labarin kaddamar da reshen jami'ar a kasashen yammacin turai da Amerika da zummar yada addinin Musulunci kamar yadda mazauna kasashen yammacin Turai da Amerika ke bukata.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Muhattatul Masar ya watsa rahoton cewa; Ahmad Khatib Shekhul Azzahar ya bada labarin kaddamar da reshen jami'ar a kasashen yammacin turai da Amerika da zummar yada addinin Musulunci kamar yadda mazauna kasashen yammacin Turai da Amerika ke bukata. Ahmad Khatib dangane da wannan labari ya bayyana cewa; burin kaddamar da jami'ar shi ne yadda addinin Musulunci da kuma abubuwa na addinin Musulunci da yada hukumce-hukumcen addini ga wadanda ba musulmi ba daga cikin al'ummomin yammatin Turai.

696171