IQNA

Yara Kanana Musulmi Na malaishiya Za Su Tafi Ziyarar Addini

Bangaren kasa da kasa; daga ranar sha tara zuwa ashirin da daya ga watan Azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya yara kanana musulmi a kasar malaishiya za su ziyarci masallacin n kasar a birnin Kalalampur fadar mulkin kasar.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Bernama ya watsa rahoton cewa; daga ranar sha tara zuwa ashirin da daya ga watan Azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya yara kanana musulmi a kasar malaishiya za su ziyarci masallacin n kasar a birnin Kalalampur fadar mulkin kasar. A ranar daya ga wannan wata ne bangaren hulda da jama'a na masallacin kasar ta Malaishiya ya fitar da wani bayani na bayyana wannan labari da cewa wannan ziyarar addini tare da hukumar kula da bunkasar addinin Musulunci a malaishiya suka shirya ga yara da shekarunsu yake tsakanin tara zuwa sha daya.



699816