Bangaren kasa da kasa; a taron da aka bawa taken amfani da hadisi ta hanyar da na'ura da za a fara a gobe biyu ga watan Azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya da ke karkashin kasuwar baje koli ta kur'ani da hadisi da jami'ar Almustapha (SAW) al'alami ta shirya a birnin Qum.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; a taron da aka bawa taken amfani da hadisi ta hanyar da na'ura da za a fara a gobe biyu ga watan Azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya da ke karkashin kasuwar baje koli ta kur'ani da hadisi da jami'ar Almustapha (SAW) al'alami ta shirya a birnin Qum. Wannan zama za a fara gudanar da shi ne bayan sallatar sallolin Magariba da Isha'I karkashin jagorancin hujjatul Islam walmuslim Bahrami shugaban bangaren Hadisi a mu'assisar ilimi mai zurfi ta imam Khomeini ®. Burin gudanar da wannan taro shi ne fadakarwa da fahimtar da al'umma irin alfanon da ke tattare da hakan da kuma yadda za a iya amfani da na'ura da ilimin zamani wajen ciyar da addini da ilimomin addini gaba.
699684