Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta icimb ya watsa rahoton cewa; a karon farko za a gudanar da taron kasa da kasa kan kasuwanci da saye da sayarwa a Musulunci daga ranekun takwas da tara ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a Kalalampur babban birnin kasar malaishiya. Wannan taro karamar jami'ar kasuwanci da lissafi ta jami'ar Malaya tare da hadin guiwar kolejin kasuwanci ta Faransa ESSEC da kuma karamar jami'ar ilimi ta birnin Zurikh na kasar Suis suka shirya.
699669