Bangaren kasa da kasa; Adadi mai yawa na marubutan kasar Turkiya sun nuna adawarsu a fili kan kasancewar VE ES Naypal mai rubutun cin fuska kan addinin Musulunci na halartar taron majalisar marubuta na Turai da nan bad a jimawa ba za a gudanar a turkiya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta medyaradar ya watsa rahoton cewa; Adadi mai yawa na marubutan kasar Turkiya sun nuna adawarsu a fili kan kasancewar VE ES Naypal mai rubutun cin fuska kan addinin Musulunci na halartar taron majalisar marubuta na Turai da nan bad a jimawa ba za a gudanar a turkiya.Shi dai wannan taro za a gudanar da shi ne a ranekun hudu zuwa shidda ga watan azar na wannnan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a birnin Istambul na kasar Turkiya. Shi dai an agayyace shi a matsayin bako na musamman saboda littafin cin mutuncin addinin Musulunci da ya rubuta.
699637