Bangaren kasa da kasa; a ranar hudu ga watan Azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya aka nuna kammala jan aiki nan na gina kauyen masu ziyartar Imam Huseini (AS) da aka bawa sunan Madinatul Huseini (AS) kuma wannan kauye ne na musamman ga maziyarta Aba Abdallah Huseini (AS) .
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a ranar hudu ga watan Azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya aka nuna kammala jan aiki nan na gina kauyen masu ziyartar Imam Huseini (AS) da aka bawa sunan Madinatul Huseini (AS) kuma wannan kauye ne na musamman ga maziyarta Aba Abdallah Huseini (AS) . Gina irin wannan kauye zai magance matsaloli da dama da maziyarta wannan kauye ke fuskanta inda za a kawo masu sauki ta fuskoki da dama iri iri musamman maziyarta da ke fitowa daga nesa da yankin na karbala'a mana'a daga jahohi daban daban na kasar ta Iraki da kuma musamman wadanda ke fitowa daga wajen kasar ta Iraki.
701632