Bangaren kasa da kasa; a karo na hamsin da hudu za a bada horo da ilmi ga masu yada addinin Musulunci da limaman masallatai a Saudiya da kuma aka fara a yau shidda ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Nasij ya watsa rahoton cewa; a karo na hamsin da hudu za a bada horo da ilmi ga masu yada addinin Musulunci da limaman masallatai a Saudiya da kuma aka fara a yau shidda ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya.Wannan bada horo zai ci gaba har zuwa ranar sha bakwai ga wannan wata da babbar cibiyar kula da limaman masallatai da masu yin huduba a jami'ar Taiyiba ta Madina ta dauki nauyin gudanarwa tare da hadin guiwar jami'ar Albaha.
701718