Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta kungiyar hadin kan kasashen musulmi OCI ya watsa rahoton cewa; Ikmalul Dine Ihsan Uglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya yi Allah wadai da shirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na gina matsugunnan yahudawa a Kudus Mai tsarki da fadada katangar Albarak . Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila dai duk da kiraye-kiraye da kashedin da ake yi mata kan wannan mummunan mataki nata na gina matsugunnan yahudawa na ci gaba da yin kunnan uwar shegu a kai.
701676