Bangaren kasa da kasa; Komitin bin diddigi da taimakekkeniya karkashin yan uwantaka da abuttaka na kungiyar hadin kan kasashen musulmi OCI a ranar shidda ga watan Aazar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya ta isa yankin zirin gaza a wani kokari na tattaunawa da mutanen yankin domin ganin yadda za su taimaka masu.