IQNA

Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Yi Allah Wadai Da Gwamnatin HKI

13:11 - November 29, 2010
Lambar Labari: 2039568
Bangaren kasa da kasa; kungiyar hadin kan kasashen larabawa a ranar shidda ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya sun yi Allah wadai da hare haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kai wa al'ummar Palasdinu fararen hula da ruguza masu gidaje a yammacin kogin jodan da Kudus mai tsarki.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Koweiti Kuna ya watsa rahoton cewa; kungiyar hadin kan kasashen larabawa a ranar shidda ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya sun yi Allah wadai da hare haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kai wa al'ummar Palasdinu fararen hula da ruguza masu gidaje a yammacin kogin jodan da Kudus mai tsarki.Muhammad Sabih mukkaddashin babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen labarai larabawa da kula da harkokin Palsdinu da mamaye ya yi Allah wadai da matakan da haramtacciyar kasar Isra'ila ta dauka kan Palasdinu.

702746

captcha