Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga jaridar Nation da ake bugawa a kasar Pakistan an bayyana cewa, An gabatar da daftarin doka da ke neman amincewar majalisar dokokin kasar Pakistan kan mallakar lasisin sayar da kayayyakin abinci na halal a kasar a ta Pakistan.
Kakakin majalisar dokokin kasar Fahmideh Mirza ta bayyana cewa, a karon farko an fara gudanar da taron baje koli na kayyakin abin cin halal a kasar Pakistan a birnin Karachi, wanda hakan ya sanya aka fara tunanin bayar da lasisi ga 'yan kasuwa domin sayar da irin wadannan kayayyaki a shagunansu.
Ta kara da cewa aiwatar da wannan shiri zai kara habbaka tattalin arzikin kasar ta Pakistan, kasantuwar kasar kasa mai muhimmanci a cikin kasashen musulmi, da matsayin a yankin da kasashen musulmi suka fi yawan al'umma.
706797