IQNA

Shirin Bayar Da Horo Kan Tafiyar Da Harkokin Kudi A Musulunci A Malazia

12:54 - December 08, 2010
Lambar Labari: 2044615
Bangaren kasa da kasa, Za a shirya gudanar da wani taro na bayar da horo kan tafiyar da harkokin kudi a mahangar addinin muslunci a kasar Malazia, wanda za a gudanar a cikin bababn otel din nan Kuwality na birnin Kualalampour.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na alafalah-consulting na yanar gizo an bayyana cewa, za a shirya gudanar da wani taro na bayar da horo kan tafiyar da harkokin kudi a mahangar addinin muslunci a kasar Malazia, wanda za a gudanar a cikin bababn otel din nan Kuwality na birnin Kualalampour fadar mulkin kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro zai samu halartar daraktoci dam asana gami da jami'ai daga ma'katu gami da cibiyoyin kudi da kuma malaman jami'a, da kuma msu nazari kanharkokin cinikayya da lamurran banki hard a masu saka hannyen jari.

Taron dai zai mayar da hanaklai ne kan yadda muslunci ya tsara harkokin cinikayya da saye da sayarwa, da kuma yadda ake saka hannayen jari. Ba'ada bayan haka kuma za a tatatuna lamurra da suka shafi harkokin banki a kasashen musulmi.

707478











captcha