IQNA

A Bahrain An Kaddamar da Bude Hauzar Ilimi Ta Gadir

Bangaren kasa da kasa:hauzar Ilimi ta Gadir aka bude a garin Satra na kasar Bahrain tare da halartar tawaga mai girma ta komitin malamai na yan shi'ar wannan kasa.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta komitin yan shi'ar kasar ta Bahrain ya watsa rahoton cewa: hauzar Ilimi ta Gadir aka bude a garin Satra na kasar Bahrain tare da halartar tawaga mai girma ta komitin malamai na yan shi'ar wannan kasa.Daga cikin manyan malamai da suka halarci gurin wannan bukin bude wannan Hauzar ilimi akawai Allama Said Jawad Alwida'I da Alama Said Abdullahi Algarifi da sheik Muhsin Algarifi sa Seikh Ja'afar Shahabi da said Abas Shabar da Sheikh Muhammad Hasan Alkarani da Seheik Said Almadih da kuma Said Majid Mush'al shugaban komitin malaman shi'a a Bahrain.

708134