Bangaren kasa da kasa;Kamal Kabtan shugaban babban masallacin birnin Liyon na kasar faransa ya bukaci da a kara bawa gurare masu tsarki da cibiyoyin addini da masallatai kariya daga hare-haren da ake kai masu da kuma a samar da wata hanya ta basu kari da kara basu goyan baya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa AFP ya watsa rahoton cewa; Kamal Kabtan shugaban babban masallacin birnin Liyon na kasar faransa ya bukaci da a kara bawa gurare masu tsarki da cibiyoyin addini da masallatai kariya daga hare-haren da ake kai masu da kuma a samar da wata hanya ta basu kari da kara basu goyan baya. Shugaban wannan babban masallaci a lokacin da yake gabatar da wani bayani ne ga manema labarai da suka ziyarce shi ya bayyana cewa: shugabannin addinai da wakilan kungiyoyi masu yaki da nuna wariyar launin fata da ta addini a yau ya kamata su tashi domin yakar wannan dabi'a ta kai wa guraren addini hare-hare da kuma ba wa irin wadannan gurare kariya.
709937