Bangaren kasa da kasa, Ya kamata mahardata kur'ani mai tsarki su zama babban abin koyi a cikin rayuwar mutane ta zamantakewa, tare da koyar da ala'da ta addinin muslunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da daya daga cikin mahardata kur'ani mai tsarki daga kasar Bosnia Sananaddin Tatarvich ya bayyana cewa, ya kamata mahardata kur'ani mai tsarki su zama babban abin koyi a cikin rayuwar mutane ta zamantakewa, tare da koyar da ala'da ta addinin muslunci.
Ya ce kura'ni mai tsarki yana koyar dad an adam yadda hakinin rayuwa take a kan haka ya kamata mahardata kur'ani mai tsarki su zama babban abin koyi a cikin rayuwar mutane ta zamantakewa, tare da koyar da ala'da ta addinin muslunci kamar yadda ya koyar.
Bosnia dai daya ce daga cikin kasashen turai, amma mafi yawan mutanen da suke rayuwa a cikin kasar mabiya addinin muslunci ne, da suke yin riko gwargwadon iko da koyarwar addinin muslunci, duk kuwa yanayin da suke ciki.
709929