IQNA

Ayatullahi Kablan Ya Jaddada Karfafa Hadin Kan Al'ummar Labanon

Bangaren kasa da kasa :Ayatullahi Kablan mukaddashin shugaban majalisar koli ta musulmin yan shi'a a kasar Labanon a ranar alhamis ashirin da biyar ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da tamanin da tara hijira shamsiya a lokacin day a ke gabatar da jawabin a ranar ashura ya bukaci dukan bangarori na siyasa da na addini a Labanon da su kiyaye hadin kai a tsakani.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta ilubnan ne ya watsa rahoton cewa; Ayatullahi Kablan mukaddashin shugaban majalisar koli ta musulmin yan shi'a a kasar Labanon a ranar alhamis ashirin da biyar ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da tamanin da tara hijira shamsiya a lokacin day a ke gabatar da jawabin a ranar ashura ya bukaci dukan bangarori na siyasa da na addini a Labanon da su kiyaye hadin kai a tsakani. Ayatullahi Kablan ya kara da cewa dukanmu muna rayuwa ne karkashin kasa guda it ace Labanon kuma dukanmu muna kaunar juna da zama yan uwan juna saboda haka ya kamata mu kawar da duk wani abu da zai haddasa baraka banbance banbance da kai wad a haddasa rikici a tsakaninmu da samar da wani yanayi na hadin kai da fahimtar juna a tsakanin al'ummar kasar Labanon baki daya har ila yau ya jaddada cewa bai dace bam u rika waiwaye kan bakaken abubuwan tarihi da suka faru a baya a tsakanin al'ummar Labanon sai dai fadar gaskiya cikin adalci domin samar da ci gaba mai dorewa a fadin kasar labanon.

713244