IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani Ta Kasa A Hadaddiyar Daular Larabawa

10:18 - December 20, 2010
Lambar Labari: 2050092
Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da gasar karatun kratun kur'ani mai tsarki ta kasa a kasar hadaddiyar daular larabawa a cikin watan Janairu mai zuwa, wadda za ta gudana a garin Shrajah.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran kasar hadaddiyar larabawa wam an bayyana cewa, za a gudanar da gasar karatun kratun kur'ani mai tsarki ta kasa a kasar hadaddiyar daular larabawa a cikin watan Janairu mai zuwa, wadda za ta gudana a garin Shrajah da ke kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa za a gudanar da ita ne bisa hadin gwiwa tsakanin kwamitin shirya gasa na kasa da kuma cibiyar raya harkokin kur'ani da sunna ta kasa, wadda take da babban mazauni a birnin Sharjah.

Wannan gasar kur'ani mai tsarki za ta samu halartar mahardata da kuma makaranta na kasar, wadanda yanzu haka suka fara gudanar da rijistar sunayensu a wurin kwamitin da ke daukar nauyin shirya gasar.

714828




captcha