Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani zaman taro kan addinin muslunci da kuma al'adu a nahiyar turai, wanda aka fara gudanarwa abirnin Bacelona na kasar Spain da kuma za a kammala cikin kwanaki biyu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na MAP na yanar gizo cewa, an fara gudanar da wani zaman taro kan addinin muslunci da kuma al'adu a nahiyar turai, wanda aka fara gudanarwa abirnin Bacelona na kasar Spain da kuma za a kammala cikin kwanaki biyu a kasar.
Babban sakataren kungiyr hadin kan musulmin kasashen nahiyar turai Tahir tijkani shi ne ya bayyana hakan a zaman taron da kungiyar ta shirya gudanarwa a kasar ta Spain, masana da dama daga cikin kasar ne da kuma kasashe daban-daban na nahiyar turai, wanda kuma za su hada da musulmi da wadanda ba musulmi ba.
Fara gudanar da wani zaman taro kan addinin muslunci da kuma al'adu a nahiyar turai, wanda aka fara gudanarwa abirnin Bacelona na kasar Spain da kuma za a kammala cikin kwanaki biyu.
714690