IQNA

An Sake Bude Tashar Radio Kur'ani A Garin Nablus Da Ke Palastaine

10:19 - December 20, 2010
Lambar Labari: 2050101
Bangaren kasa da kasa, An sake bude tashar radiyon nan ta radio kur'an da ke watsa shirye-shiryenta kan kur'ani mai tsarki daga birnin Nablus a yankin Palastine, bayan da bababr kotun koli ta palastine ta yanke hukunci kan hakan.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ma'a an bayyana cewa, An sake bude tashar radiyon nan ta radio kur'an da ke watsa shirye-shiryenta kan kur'ani mai tsarki daga birnin Nablus a yankin Palastine, bayan da bababr kotun koli ta palastine ta yanke hukunci.

Bayanin ya ci gaba da cewa ma'aikatar yada labarai ta palastine ta bayyana cewa tun kafin wannan lokacin ta yi matukar kokari wajen ganin ta hada kan dukkanin kungiyoyin 'yan jarida da kafofin sadarwa, domin ganin an bi hanyoyi na shari'a domin dawo da gidan radiyo kur'an.

Wannan gidan radiyo yana watsa dadaden shirye-shirye da suka danganci kur'ani mai tsarki daga birnin na Nablus, kuma shi ne gidan radiyon da ked a masu saurare fiye da kowanne a yankin.

714545



captcha