IQNA

Kafa Cibiyar Ilimi Ta Musamman Ga Tattalin Arziki ta Musulmi A Imarat

Bangaren kasa da kasa; a karon farko a birnin abu zabin fadar mulkin hadeddiyar daular larabawa za kafa cibiyar ilimi ta musamman ta tattalin arziki a mahangar Musulunci da kyakkyawan dabi'u ta yankin gabas ta tsakiya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga jaridar Hadeddiyar daular larabawa Albayan ya watsa rahoton cewa; a karon farko a birnin abu zabin fadar mulkin hadeddiyar daular larabawa za kafa cibiyar ilimi ta musamman ta tattalin arziki a mahangar Musulunci da kyakkyawan dabi'u ta yankin gabas ta tsakiya. Burin kafa wannan cibiyar ta bada horo shi ne daukakawa da fadada ilimi da bincike a tsakanin al'ummar musulmi da kuma wannan manufa.

714380