IQNA

Za A Gudanar Da Wani Shiri Bayar Da Horo Kan Sallah A Belgium

16:48 - December 21, 2010
Lambar Labari: 2050647
Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da wani na koyar da sallah wanda zai kebanci kanan yara da kuma matasa a birnin birnin Brussel fadar mulkin kasar Belgium.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islamic-event an bayyan acewa, za a gudanar da wani na koyar da sallah wanda zai kebanci kanan yara da kuma matasa a birnin birnin Brussel fadar mulkin kasar Belgium da day ace daga cikin kasashe mambobi a kungiyar tarayyar turai.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shiri na bayar da horo yana daya daga cikin irin shirye-shiryen da babbar cibiyar yada addinin muslunci ta kasar ta saba gudanarwa, da nufin kara fahimtar da musulmi hakikanin addininsu, ta yadda za su iya isar da shi ga wasu.

Taron bayar da horon dai zai kwashe kwanaki hudu ana gudanar da shi, inda masana da malamai musulmi za su gababtar da jawabai na kara kawar da kan matasa dangane da koyarwar addinin muslunci.

715111



captcha