IQNA

Taron Baje Kolin Kayayyakin fasahar Musulunci A Birnin Munich

16:48 - December 21, 2010
Lambar Labari: 2050649
Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da wani baje kolin kayayykin fasahar muslunci a birnin Munich na kasar Jamus, inda ake nuna kayan al'adu na kasashen musulmi da kuma dadaddiyar fasaharsu.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, awani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na Oslam today an bayyana cewa, an fara gudanar da wani baje kolin kayayykin fasahar muslunci a birnin Munich na kasar Jamus, inda ake nuna kayan al'adu na kasashen musulmi da kuma dadaddiyar fasaharsu ta asali.

Bayanin ya ci gaba da cewa daga cikin abubuwan da ake nunawa awajen baje kolin har da kayayyakin da suka jima na tsawon daruruwan shekaru, haka nan kuma adadiin ababen da aka nuna sun kai kimanin talatin.

Musulmi da suke rayuwa a cikin kasashen turai suna kokarin ganin sun wayar da kan sauran mutane da suke rayuwa tare da su, wadanda akasarinsu ba mabiya addinin Musulunci ne ba kan addinin muslunci da koyarwarsa.

715094



captcha