IQNA

An Kammala Bayar Da Horon Karatun Karatun Kur'ani A Hadaddiyar Daular Larabawa

16:47 - December 21, 2010
Lambar Labari: 2050651
Bangaren kasa da kasa, An kawo karshen shirin nan na bayar da horo kan karatun kur'ani mai tsarki a kasar hadaddiyar daular larabawa a birnin Dubai cibiyar kasuwancin kasar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin kamfanin dillancin labaran kasar hadaddiyar daular larabawa wam cewa, an kawo karshen shirin nan na bayar da horo kan karatun kur'ani mai tsarki a kasar hadaddiyar daular larabawa a birnin Dubai cibiyar kasuwancin kasar ta UAE.

Wadanda suka jagoranci gudanar da wannan shiri sun tabbatar da cewa wakilan cibiyoyin kur'ani sama da dari daya daga sassa daban-daban na kasar ne suka halarci wannan bayar da horo, inda suka koyar da yara karatu da kuma ka'idojinsa.

Shugaban kwamitin da ya jagoranci aiwatar da shiri ya bayyana cewa, gudanar da wannan bayar da horo shiri na fuskantar tarukan gasar karatu da hardar kur'ani ne da za a gudanar a nagaba a kasar.

715050




captcha