Bangaren siyasa ; Yunaton Batnatan wakilin kiristoci a majalisar dokokin jamhuriyar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa; halartar kiristoci a taron juyayin tasu'a da ashura na Imam Huseini (AS) wata babbar alama ce da muhimmancin da kiristocin ke bawa wannan bawon Allah da kuma iitikadin na bai daya tsakanin kirsitoci da musulmi a bangare guda kuma hadin kai a tsakanin al'ummar kasa.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa : Yunaton Batnatan wakilin kiristoci a majalisar dokokin jamhuriyar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa; halartar kiristoci a taron juyayin tasu'a da ashura na Imam Huseini (AS) wata babbar alama ce da muhimmancin da kiristocin ke bawa wannan bawon Allah da kuma iitikadin na bai daya tsakanin kirsitoci da musulmi a bangare guda kuma hadin kai a tsakanin al'ummar kasa. Wakilin na kiristoci a majalisar dokokin jamhuriyar Musulunci ta Iran ya fadi haka ne a wata tattaunawa da ta gudana tsakaninsa da kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran inda ya yi nuni da yadda kiristoci suka taka rawa wajen kula da tsaron lafiyar Imam Huseini (AS) da kuma juyayi kan shahadarsa.
715103