Bangaren kasa da kasa:An bayyana lokacin gasar kasa da kasa karo na tara na kyautar shugaban kasar Tunusiya dangane da nazarin Musulunci a shekara ta dubu biyu da goma.
Kamfanin dillancin labarai da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar jaridar kasar Jodan Alraayi ya watsa rahoton cewa; An bayyana lokacin gasar kasa da kasa karo na tara na kyautar shugaban kasar Tunusiya dangane da nazarin Musulunci a shekara ta dubu biyu da goma. Ma'aikatar da ke kula da harkokin addini a wannan kasa ta Tunusiya a cikin wannan sanarwa da ta fitar a ranar ashirin da tara ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara ta bayyana cewa; a cikin wannan gasa akwai manazarta dam asana da dama da suka bayyana aniyarsu da halartar wannan gasar.
715820