IQNA

A Karon Farko An Kafa Mu'assisar Tattalin Arziki Da Akhalaki Ta Musulunci

Bangaren kasa da kasa ; a karon farko a Hadeddiyar Daular Larabawa an kafa da kaddamar da mu'assisar tattalin arziki da kyawawan dabi'u na Musulunci ta yankin gabas ta tsakiya da bankin Musulunci ta Abu Zabi (ADIB) da ke Hadeddiyar daular Larabawa.

Kamfanin dillancin labarai da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta WAM ya watsa rahoton cewa; a karon farko a Hadeddiyar Daular Larabawa an kafa da kaddamar da mu'assisar tattalin arziki da kyawawan dabi'u na Musulunci ta yankin gabas ta tsakiya da bankin Musulunci ta Abu Zabi (ADIB) da ke Hadeddiyar daular Larabawa. Kafa wannan mu'assisar ko shakka babu zai tabbata da yadda musulmi suka himmatu da kuma yadda kafa irin wannan mu'assisar zai taimaka matuka gaya ta fuskar ilimi da harkokin tattalin arziki day a yi daidai da mahangar Musulunci da kuma kyawawan dabi'u irin na Musulunci .


715287