Bangaren kasa da kasa, Wasu daga cikin masu adawa da yaduwar addinin muslunci a cikin kasashen yammacin turai suna gudanar da tarjamar kur'ani mai tsarki da nufin buce hasken addinin muslunci a cikin yammacin turai.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, wani dalibin jami'a a kasar Birtaniya da ya kammala digiri na biyu ya sheda cewa, wasu daga cikin masu adawa da yaduwar addinin muslunci a cikin kasashen yammacin turai suna gudanar da tarjamar kur'ani mai tsarki da nufin buce hasken addinin muslunci a cikin yammacin turai musamman ma masu magana da harshen ingilishi.
Dalibin wanda ya rubuta littafi kan tarjama da rabe-rabenta, wanda kuma shi ne abin da ya karanta kuma yak ware a kansa, ya tabbatar da cewabisa la'akari da yadda wasu suke gudanar da tarjama kur'ani za a iya fahimtar cewa manufarsu ita ce bakantar surarsa.
Ya yi kira ga dukkanin masu gudanar da ayyykan tarjama da su san cewa mutuncinsu shi ne kare aikinsu, kuma juya manufa a lokacin gudanar da tarjama ya sabawa dukkanin ka'idoji da dokoki na tarjama daga wani yare zuwa wani.
715913