IQNA

An Girmama Daliban Da Suka Gudanar Da Gasar Kur'ani A Canada

16:00 - December 22, 2010
Lambar Labari: 2051863
Bangaren kasa da kasa, an girmama daliban da suka gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki a kasar Canada, wadda cibiyar bunkasa ilmomin kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na cibiyar yada ilmomin kur'ai ta duniya an bayyana cewa, an girmama daliban da suka gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki a kasar Canada, wadda cibiyar bunkasa ilmomin kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a kasar ta Canada.

Wanna gasar hardar kur'ani na daya daga cikinta da aka gudanar a matsayi na kasa da kasa da ta samu karbuwa matuka daga al'ummar musulmi mazaun akasar Canada, an ka girmama dukkanin wadanda suka shiga gasar, musamman ma wadanda suka a mataki na daya da na biyu da na uku.

An gudanar da gasar ne ababban dakin gudanar da taruka na brnin Tronto fadar mulkin kasar Canada, tare da halartar wakilan kungiyoyin musuli na kasar da wasu kasashen musulmi.

715909




captcha