IQNA

Taro Kan Bahasi Dangane Da Ci gaban Al'adun Musulunci

16:59 - December 23, 2010
Lambar Labari: 2052122
Bangaren kasa da kasa, Wadanda suka halarcin zamn taro a birnin Barcelona nakasar Spain mai taken Musulunci da aladun turai, sun amince kan cewa dole musulmin da ke rayuwa a cikin kasashen nahiyar su samu 'yancin gudanar da ayyukansu na ibada.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na morocjournal an bayayana cewa, wadanda suka halarcin zamn taro a birnin Barcelona nakasar Spain mai taken Musulunci da aladun turai, sun amince kan cewa dole musulmin da ke rayuwa a cikin kasashen nahiyar su samu 'yancin gudanar da ayyukansu na ibadarsu daidai da koyarawar musulunci.
A cikin bayanin bayan taro da dukkanin mahalarta taron suka amince da shi kuma a fitar da shi, an jaddada muhimmancin gudanar da tatatunawa tsakanin mabiya addinai musamman ma dai wadanda aka safkar daga sama domin kara samun fahimtar juna.
Daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai a wajen taron dai akwai malaman jami'oi da kuma malaman addinin muslunci gami dam asana daga sassa daban-daban na kasashen turai da na musulmi.
716789
captcha