Bnagaren kasa da kasa, Za a gudanar da wani zaman taro a cikin wannan wata na disemba abirnin Paris fadar mulkin kasar Faranasa mai taken alamun abincin halal ga musulmi, wanda kungiyoyin musulmi na kasar za su dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dillanci labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na foodlabel-institute na yanar gizo an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro a cikin wannan wata na disemba abirnin Paris fadar mulkin kasar Faranasa mai taken alamun abincin halal ga musulmi, wanda kungiyoyin musulmi na kasar za su dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin makonni biyu masu zuwa.
Wadanda suka dauki shirya wannan zaman taro sun bayyana cewa manufar tarin dai ita ce kara waya da kan musulmi musamman ma dai wadanda suke zaune a cikin kasashen nahiyar turai, domin sanin abinci da addininsu ya yarje musu su cid a wanda ba a yarje musu ba.
A yayin gudanar taron za a bukaci kamfanoni masu gudanar da ayyuka na hada kayan abinci da su su rika saka wata alama da za ta iya tabbatar wa musulmi cewa abinci na halal net a yadda musulmi za su iya saye hankali kwance.
716849