IQNA

Sabon Rahoto Kan Killace Zirin Gaza Ba Kan Ka'ida Ba

16:49 - December 25, 2010
Lambar Labari: 2052982
Bangaren kasa da kasa;Cibiyar bincike kan take hakkin dan adam a Palasdinu ta fitar da wani sabon rahoto kan killace yankin zirin gaza ba kan ka'ida da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Ma;a ya watsa rahoton cewa: Cibiyar bincike kan take hakkin dan adam a Palasdinu ta fitar da wani sabon rahoto kan killace yankin zirin gaza ba kan ka'ida da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi. A cikin wannan rahoto an yi bayani dalla-dalla kan mummunan tasirin da killacewar yankin ta jawowa mutanan Zirin Gaza da Haramtacciyar kasar Isra'ila ke zaluntar mutanan Gaza.Tun shekara ta dubu biyu da hudu ne Gaza ta fada karkashin mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kuma bayan haka suka ci gaba da muzgunawa mutanan yankin.

717398
captcha