Bangaren kasa da kasa; Taro dangane da imam Huseini (AS) a mahangar musullunci da kiristoci da aka gudanar a ranar biyu ga watan Dai na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya. Cibiyar Musulunci da al'adu da ke karkashin kungiyar agaji ta Almubarrat ta Labanon da ke masallacin Imamain Hasanain a birnin Beirut fadar mulkin kasar Labanon aka gudanar da wannan taro.