Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Libya ta girmama makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki da suka yi kwazo a dukkanin gasar da aka gudanar a cikin shekara ta 2009 a mataki na kasa da kuma mataki na kasa da kasa.
Kamfanin dillancin labaran kqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na na yanar gizo na jaridar Alfajrul jaded an habarta cewa, gwamnatin kasar Libya ta girmama makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki da suka yi kwazo a dukkanin gasar da aka gudanar a cikin shekara ta 2009 a mataki na kasa da kuma mataki na duniya.
Rahoton ya ci gaba da cewa an gudanar da gagarumin zaman taro na girmama makarntan da kuma mahardatan a birnin Tripoli fadar mulkin kasar, tare da halartar wasu daga cikin jami'an gwamnati da kuma wakilan cibiyoyin muslunci musamman ma na kur'ani.
Gwamnatin kasar Libya tan a bayar da muhimmanci da girmama makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki da suka yi kwazo a dukkanin gasar da aka gudanar a cikin shekara ta 2009 a mataki na kasa da kuma mataki na kasa da kasa.
718042